Labaran garkuwa da mutane
Hukumar da ke kula da harkokin matasa masu yiwa ƙasa hidima a Najeriya NYSC ta ayyana ɓatan kodinetan da ke kula da jihar Akwa Ibom tare da direbansa.
Yayin da rashin tsaro ya ke kamari, an gano yadda gwamnatin tarayya ta fitar da kudi masu nauyi domin yakar ta'addanci a sassan da ta'addanci ya yi katutu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi, Barista Dare.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yiwa jami'an rundunar tsaron jihar Sokoto kwanton bauna. 'Yan bindigan sun hallaka mutum biyar tare da wasu manoma.
Gwamnonin Arewa ta yamma sun shirya taron zaman lafiya a Kaduna domin ba kwamishinonin tsaro horo kan yaki da yan bindiga. Gwamnan Kaduna ya kaddamar da taron.
Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarat hallaka ƙasurgumin ɗan ta'adda aka jima ana nema ruwa a jallo, sun kwato makamai bayan musayar wuta a Taraba.
Gwamnatin jihar Sokoto ta raba tallafi Naira Miliyan 10 da tirelolin abinci ga mazauna karamar hukumar Isa da rashin tsaro ya hana su sakewa domin rage radadin.
Yan fashin daji sun kai hari tare da garkuwa da sarkin Gobir Isa Bawa da ɗansa a hanyarsu ta komawa gida a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato.
Wasu tsagerun ƴan bindiga sun hallaka mutum 5 ƴan gudun hijira a masallaci a kauyen Katapko da ke yankin ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa ranar Alhamis.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari