Labaran garkuwa da mutane
Sojojin Najeriya sun kama yaran ƙasurgumin ɗan bindiga Veior John Gata bayan musayar wuta a jihar Taraba. Sojoji sun kwato makamai da babura da dama.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne. Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai a hannunsu.
'Yan banga da mafarauta sun kashe ‘yan bindiga yayin wani artabu a dajin Achido, sun kuma ceto mutane 14, ciki har da Abdullahi da aka sace makonnin baya.
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace mutane sama da 100 a Zamfara. Cikin waɗanda aka sace akwai mata, yara ƙanana da limamin garin aka tafi da su.
Yan sanda sun yi gumurzu wajen ceto matafiya 19 da aka sace a jihar Neja. Matafiyan sun fito ne daga jihar Sokoto zuwa Bayelsa kuma an mayar da su gida.
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace mutane 22 da suka tare motoci biyar a titin zuwa Kontagora ranar Alhamis.
Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD ta ƙasa, Tope Zenith Osundara, ya tabbatar da dawowar likitar da aka yi garkuwa da ita tun Disamɓa.
Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani dan kasuwa a jihar Ebonyi. Yan bindigar sun harbe dan kasuwar tare da ƙona gawarsa a cikin gidansa.
Maharan da suka yi garkuwa da limamin coci a jihar Edo sun tuntuɓi ƴan uwansa sun bukaci lale masu kudi fansa Naira Miliyan 200 kafin da su sake shi.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari