Jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tuna da 'yan majalisar dokokin jihar yayin da ya gwangwaje su da sabbin motoci. Gwamnan ya ce yana so su ji dadin yin aiki.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta kammala shirye-shirye don samar da wutar lantarki na awanni 24 a lokacin azumin Ramada.
Yayin da 'yan Najeriya ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, Sarkin Gwandu ya shawarci ‘yan kasuwa kan jin tsoron Allah a kasuwancinsu na siyar da kaya.
Cibiyar kula da cututtuka ta Jihar Kebbi (EOC), ta sanar da jama’a game da bullar cutar murar tsuntsaye a wasu sassa na jihar kuma har kashe tsuntsaye a Amanawa.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu, ta kulle manyan makarantun kuɗi guda biyu kan ƙin biyan hakkin gwamnati.
Gwamna Nasiru Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewa gwamnatinsa zata ciyar da jama'a abinci kyauta a watan Ramadan domin neman ladan Allah madaikakin sarki.
Gwamna Nasir Idirs na jihar Kebbi ya sanar da rusa dukkan ciyamomin kananan hukumomi 21 a jihar inda ya yi alkawarin ba zai ya da su ba a harkokin gwamnatin jihar.
Gwamnatin jihar Kebbi tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya sun shirya farfado da harkar noma a jihar. Gwamnatin za ta ba manoman rani man fetur kyauta.
Akalla 'yan mata, zawarawa da marasa galihu 300 ne aka aurar da su ga masoyansu wanda gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyin yi, bayan kashe sama da naira miliyan 21.
Jihar Kebbi
Samu kari