Jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi ya ce ba a yi maganar dawo da tallafin man fetur ba a zaman majalisar magabatan kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa a ranar Talata.
Majalisar Matasan Arewa ya yi tir da bukatar da wasu mutane ke yi na gwamnati ta sauyawa cibiyar fasaha ta hukumar sadarwa matsuguni zuwa jihar Kebbi.
Ministan kasafi da tsare-tsare, Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa kwata-kwata albashinsa bai kai ko miliyan daya ba inda ya ce mutane ne suke zarge-zarge.
Bayan fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Najeriya, an samu mutuwar mutane 14 a jihohin Kaduna, Borno, Niger da Kebbi dukkansu a Arewacin Najeriya.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a sansanin jami'an hukumar kwastam a jihar Kebbi. Sun hallaka jami'i daya tare da sace wani jami'in.
'Yan majalisar jiha a Kebbi sun bayyana sauya sheka zuwa APC a daidai lokacin da ake ci gaba da kuka da yadda jam'iyyar APC ke yiwa 'yan kasar nan gashi.
'Yan majalisar dokokin jihar Kebbi guda uku da aka zaba a inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar. Sun samu tarba mai kyau.
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya kori dukkan shugabannin riko na kananan hukumomi 21 a jihar yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a watan Agustan 2024.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajantawa Sanata Bala Ibn Na'Allah bayan rasuwar matarsa mai suna Safiya Na'Allah da yammacin jiya Talata.
Jihar Kebbi
Samu kari