Katsina
Allah ya karbi rayuwar shugaban cibiyar nazari da bunkasa Ilimi ta kasa (NERDC), Farfesa Ismail Junaidu a yayin da ya ke halartar taron kwamitin tuntuba kan ilimi.
Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamiti da zai binciki jami'an hukumar Hisbah bisa kisan wani mai sana'ar faci a yayin wani bikin aure bayan sun kai samame.
Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya mika godiya ga Bola Tinubu kan aikin hanya da ya kawo musu a jihar da za ta kawo saukin rayuwa.
Masu sana'o'i a mazabar Musawa/Matazu da ke jihar Katsina sun samu tagomashin tallafi daga dan majalisarsu, Abdullahi Ahmed Aliyu da zummar bunkasa sana'arsu.
Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Umaru Radda ta kirkiro dokar hutun iddah domin bai wa matan da mazansu suka rasu hutun wata huɗu da kwana 10.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International (AI) ta shawarci gwamnatin tarayya kan yadda za ta bullowa lamarin zanga-zanga a kasar nan.
Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ta godewa ɗaukacin al'ummar da suka taimaka da addu'a lokacin da aka sace ta.
Mazauna karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, sun fito kan tituna domin nuna adawarsu da yadda 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka a yankin.
Hukumar Hisbah reshen jihar Katsina ta bayyana kamawa da lalata kwayoyi da giya da suka kai darajar miliyan sittin a karamar hukumar Funtua dake jihar.
Katsina
Samu kari