Katsina
Kamfanin raba wuta na Kano watau KEDCO ya tabbatar da cewa an samu matsala a wata karamar tashar wuta bayan taransufoma ta kone, ya bai wa mutane hakuri.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara bayan sun farmaki 'yan bindiga a kan iyakokin Katsina da Kano. Sojojin sun hallaka 'yan bindiga da dama.
Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya ce zaman lafiya na dawowa a wasu kananan hukumomi da ‘yan bindiga suka addaba, yana sa ran 2026 za ta fi armashi.
Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya akalla guda biyar ne suka kaddamar da jami'an tsaro domin kakkabe masifar yan bindiga da suka addabi al'ummominsu.
A labarin nan, za a ji cewa wani jigo a APC reshen Jihar Katsina ya bayyana rokon gwamna Umaru Dikko Radda ya taimaka masu da hular kwano kafin kamfen.
An shiga tashin hankali a Sabuwar Unguwa da ke Katsina biyo bayan kisan wasu matasa biyu, ciki har da 'Kuda'. Matasa sun kona ofishin NSCDC da raunata 'yan sanda.
'Yan bindiga sun kulla yarjejeniya kan sulhu da mahukunta a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina. Sun sako mutanen da suka yi garkuwa da su.
Malam Yahaya Makaho ya soki sarautar Sarkin wakar kasar Hausa da aka bai wa Dauda Kahutu Rarara, yana cewa Daura ba ta wakiltar daukacin kasar Hausa.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yunkurin samar da wata runduna ta musamman da za ta rika sintiri a iyakokin jihohin Arewa maso Yamma.
Katsina
Samu kari