Kasashen Duniya
Tsohon ministan harkokin kasashen waje, Bolaji Akinyemi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan game da karbo bashi daga kasar Sin watau China.
Wani saurayi ya cinnawa budurwarsa wuta ta mutu a kasar Uganda. An tabbatar da mutuwar budurwar ne yar wasan Olympics bayan mafi yawan jikinta ya kone.
Mai kudin duniya, Bill Gates ya ce haraji da ake karba a Najeriya ya yi kadan idan ana son inganta kasa. Ya ce dole a kara haraji idan ana son inganta ilimi, lafiya
Kasar Amurka ta kwace wani jirgin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro. Amurka ta ce gwamnatin Nicolas Maduro ta karya takunkumin da ta kakaba mata.
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Birtaniya ce mafi tsadar man fetur a duniya inda ta ke sayar da lita kan N2973 yayin da Najeriya ke fama da wahalar karancin man.
Andrew Wynne, dan ƙasar Burtaniya da rundunar yan sandan kasar nan ta ce ta na nema ruwa a jallo ya musanta zargin da hukumomin Najeriya ke yi masa.
Dandalin sada zumunta na X ya daina aiki a cikin kasar Brazil mai mutane miliyan 200, sakamakon kazamin fada tsakanin Elon Musk da wani alkali dan kasar.
A wannan labarin za ku ji cewa kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta dora alhakin yawaitar fita yin aiki kasashen waje kan rashin tsaro a kasar nan.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga birnin taraya Abuja zuwa Beijin na ƙasar China, fadar shugaban kasa ta ce zai tsaya a UAE kafin ya ƙarisa.
Kasashen Duniya
Samu kari