Kasashen Duniya
A Afirka, wasu daga cikin shugabannin kasashen nahiyar sun shafe shekaru da dama suna rike da madafun iko yayin da kuma suka haura shekaru 70 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa Alkahira da ke kasar Masar ce babban birni mafi bunkasa a yawan jama'a a Afrika. Wannan kididdigar an sameta daga Majalisar Dinkin Duniya.
Gwamnatin Saudiyya ta nada limamai a masallacin Makka da masasallacin Manzon Allah SAW a Madina. Limaman za su rika jan sallah a masallatan da ayyukan addini.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga 'yan Najeriya mazauna Lebanon da su dawo gida bayan da tashe tashen hankula suka kara ta'azzara a Gabas ta Tsakiya.
Iran ta kai hare haren Isra'ila a ranar Talata. Harin da Iran ta kai Isra'ila ya biyo bayan kashe shugaban Hamas da Hisbullah ne da Isra'ila ta yi a kwankin baya.
Benjamin Netanyahu, firaministan Isra'ila, ya bayyana kisan da aka yi wa Hassan Nasrallah, sakatare-janar kuma shugaban kungiyar Hizbullah, a matsayin ramuwar gayya.
Binciken da aka yi a kan ikirarin Aliko Dangote ya nuna cewa akwai rashin gaskiya a kan cewa man fetur ya fi arha da 40% a Najeriya fiye da a kasar Saudiya
An kama mutane uku da zargin kitsa juyin mulki ga shugaban kasar Benin. An kama kwamandan sojoji, ministan wasanni da wani babban dan kasuwa a kasar.
Saudiya ta ce ba za ta daina kokarinta na neman 'yancin kasar Falasdinu ba, kuma ba za ta kullawata alaka ta diflomasiya da Isra'ila har sai an cimma hakan.
Kasashen Duniya
Samu kari