
Kasashen Duniya







Saudiyya ta karyata rahoton da ke cewa an hana kasashe 13 neman biza. Ta ce babu sabon takunkumi, sai dai ka’idar Hajji ga masu bizar yawon shakatawa.

Gwamnatin tarayya ta fara tantance wasu 'yan siyasa da ake shirin nada wa a matsayin jakadun Najerya bayan shafe watanni babu wakilci a kasashen waje.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dakar da ke kasar Senegal domin wakiltar Bola Tinubu a wani babban taro.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tafiya zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin yin hutun kwanaki 14. 'Yan Najeriya sun yi masa martani mai zafi.

Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kakaba harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga mambobin kasashen ECOWAS ciki har da Najeriya.

Masana falaki sun tabbatar cewa jinjirin watan Shawwal zai kasance a sararin samaniya, amma saboda matsalolin yanayi da warwatsewar haske, ba zai yiwu a gan shi ba.

Gwamnatin Birtaniya ta fitar da jerin kadarorin da wasu 'yan Najeriya 60 suka mutu suka bari, kuma har yanzu babu wani magajinsu da ya je ya karɓe su.

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya kama mataimakinsa, Riek Machar. Kasashen waje na rufe ofisoshinsu yayin da rikicin basasa ke shirin barkewa a kasar.

Shugabannin GAVI, kungiyar da ke bayar da tallafin rigakafi ka kasashe sun ce idan Amurka ta dakatar da tallafinsu, mutane miliyan 1.2 za su mutu a shekaru 5.
Kasashen Duniya
Samu kari