
Kannywood







Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ba za ta lamunci rashin tarbiyya da take dokokin addinin Musulunci da wasu 'yan Kannywood ke yi da sunan sana'a ba.

Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar jarumi Yaya Ɗanƙwambo, an yi mata sutura a Samarun Zaria. Haka zalika, Mahaifin jarumi Baba Ari ya rasu, kuma an yi masa sutura.

Hadiza Gabon ta ce 'yan mata su daina damuwa da saurayinsu kawai, su auri mijin da ya dace, ko da mijin wata ne, a cewar wani sako daga Hassan Giggs.

Shekarar ta 2025 za ta zamo shekarar da za a ga sababbin finafinan Hausa da salon daukarsu ya sha bamban da na baya. Mun zakulo finafinai 6 da za a haska a 2025.

Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, na shekara guda saboda hotuna da bidiyo na batsa da suka tada hankali.

Jaruma Radeeya Jibril ta yi aure, ta gode wa wasu 'yan masana'antar finafinan, tana mai alfahari da Kannywood, kuma ta nemi yafiya ga duk wanda ta yiwa ba daidai ba.

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta dakatar da jarumar Kannywood Samha M Inuwa saboda yaɗa bidiyoyi da hotunan da ba su dace ba a kafafen sadarwa.

Rahama Sadau ta ce Ali Nuhu ne ya gano ta tana rawa a Kaduna, ya ce duk mai iya rawa zai iya fim, ya kuma shigar da ita Kannywood. Ta ce daga nan rayuwarta ta canja.

Rahama Sadau da Umar M Shareef sun taka rawa a Kaduna don murnar sabuwar shekara. Bidiyonsu ya jawo martani masu dadi, inda jama'a ke musu addu’a da fatan alheri.
Kannywood
Samu kari