
Jihar Kaduna







Nasir El-Rufa'i ya zargi gwamnan Kaduna, Uba Sani da aiki tare da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin a dakushe tasirin siyasarsa kafin zaben 2027.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi Allah ya isa ga 'yan majalisar Kaduna kan bincikensa da ake a kan rashawa. El-Rufa'i ya ce karshensu zai yi muni.

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana yadda Uba Sani ke kashe mu raba da yan kwangila kafin ya amince ya ba su aikin gwamnatin jihar.

Tsohon gwamnan Kaduna , Nasir El-Rufai ya zargi mai ba shugaban ƙasa shawara a harkar tsaro, Nuhu Ribadu da shirya makarkashiyar tura shi gidan yari kafin zaben 2027

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya zargi magajinsa, Sanata Uba Sani da wawure kudin kanann hukumomi da sayen kadarori a ƙasashen ketare.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shahararren malamin cocin katolika na Sakkwato, Bishof Mathewa Kuka a matsayin shugaban majalir gudanar na Jami'ar Kachia.

Yan takara 200 da suka fafata a zaben kananan hukumomin jihar Kaduna tare da magoya bayansu akalla 10000 sun tattara kayansu daga NNPP, sun koma SDP.

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce ya rama miyagun maganganu da Nasir El-Rufa'i ya fada a kansa a baya.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta gamsu da kamun ludayin salon mulkin Gwamna Uba Sani. Ta ce za ta ci gaba ɗa yi masa addu'a.
Jihar Kaduna
Samu kari