Jihar Yobe
Sanatan Yobe ta Gabas, Mustapha Musa, ya janye daga sake tsayawa takarar zabe a 2027 tare da marawa Gwamna Mai Mala Buni baya a matsayin magajinsa.
Gwamna Mai Mala Buni da 'yan APC a jihar Yobe sun amince da tsohon sakataren gwamnati jihar Baba Malam Wali ya yi takarar gwamna a zaben 2027 mai zuwa.
Gwamnoni 7 na Arewa, ciki har da Zulum da Buni, za su sauka daga mulki a 2027. Legit Hausa ta yi nazarin nasarorinsu da kuma makomar siyasarsu kafin barin gado.
Jami'an rundunar sojin Najeirya sun kama wani mutumi da ake zargin dan leken asirin kungiyar ta'addancin Boko Haram ne a filin jirgin sama a jihar Yobe.
Dakarun Operation HADIN KAI sun kashe wani babban jigo a majalisar Shura ta ISWAP mai suna Abu Jarir a wani samame da suka kai a yankin jihar Yobe.
Mataimakin gwamnan jihar Yobe, Idi Gubana ya lara godewa Allah SWT bisa ni'imar da ya masa ta hanyar gina sababbin masallatai da daukar nauyin auren marayu.
Gwamnati jihar Yobe ta tara malamai 800 daga sassa daban-daban domin yi wa shugabanni addu'a. Malaman za su yi wa shugaba Bola Tinubu addu'ar nasara.
A labarin nan, za a ji cewa Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya fusata da harin sojojin sama da ya hallaka fararen hula akalla 200 a wata kasuwa da ke iyakar Borno da Yobe.
Jirgin yaƙin sojojin saman Najeriya ya kashe mutane 56 a kasuwar Jilli da ke iyakar Borno da Yobe, da tunanin cewa ƴan ta'adda ne suka taru a kasuwar.
Jihar Yobe
Samu kari