
Jihar Yobe







An samu mutanen da suka jikkata, bayan wani bam ya fashe a jihar Yobe. Lamarin ya auku ne a cikin daji bayan wani matashi yaje samo itacen girki.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dauko matasa ya ba su mukamai a cikin gwamnatinsa. Gwamna Mai Mala Buni ya nada matasa 200 a matsayin hadimansa.

Wasu 'yan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai harin ta'addanci a jihar Yobe. 'Yan ta'addan sun hallaka wani dan sa-kai tare da kona gidaje.

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari gidan jami’in ‘yan sanda a Buni Yadi, suka kashe ‘ya’yansa biyu, suka kona gawarwakinsu da gidan, lamarin ya jefa tsoro.

Rundunar 'yan sandan kasar mam ta tabbatar da cewa an samu sakaci daga wasu daga cikin jami'anta, wanda ya yi sanadiyyar batan dubban bindigun da gwamnati ta samar.

Bankin raya Afrika na AfDB ya raba tallafin abinci na Dala miliyan 1 dmin dakile fatara da yunwa a yankin Arewa maso Gabas sakamakon ambaliyar ruwa.

Daliba daya ta rasu, biyar sun jikkata sakamakon rushewar bangon aji a GGSS Potiskum, Yobe. Gwamnatin jihar ta ce za a binciki musabbabin hatsarin.

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun tafka barna a jihar Yobe. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an 'yan sanda guda biyu har lahira.

ACP Dauda Fika, jarumin dan sanda da ke yaki da Boko Haram, ya rasu a Abuja. Ya jagoranci hare-haren kwato garuruwa a Yobe da Borno daga hannun ‘yan ta’adda.
Jihar Yobe
Samu kari