Jihar Kogi
Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya bayyana cewa hadakar ADC na kara karfi a kowace rana kuma ta shirya ganin bayan APC a zaben 2027 mai zuwa.
Majalisar dattawa ta gargadi Sanata Natasha Akpoti kan cewa za ta koma bakin aiki. Majalisar ta ce har yanzu tsugune ba ta kare ba game da dakatar da ita da aka yi.
Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama zai sauka a wasu jihohin Arewa da Kudu, inda ake fargabar ambaliya za ta afku a Neja da Kogi a ranar Talata.
Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan yawan ciyo bashi da take yi, yana mai cewa za su iya neman bashi har a Opay.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da sace basaraken gargajiya na Bagaji Odo, David Wada, yayin da yake dawowa daga wani taron sarakuna.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Kogi. 'Yan bindiga sun sace basaraken ne lokacin da yake kan hanyar dawowa daga taro.
Wata dalibar ‘yar shekarar karshe a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi ta mutu a asibiti lokacin da ake kokarin raba ta da ciki wanda ya kai har na wata shida.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya amince da kirkiro karin sarakuna uku domin karfafa ayyukan masarautun gargajiya a jihar Kogi, ya dawo da sarkin Omala.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bukaci 'yan majalisar dokoki su mara wa Gwamna Ahmed Usman Ododo baya, domin ci gaban jihar gaba ɗaya.
Jihar Kogi
Samu kari