Jihar Kogi
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Abdulmalik Abdulazeez Obadaki a gaban kotu, mutumin da ake zargi da jagorantar kai hari wata coci a jihar Kogi.
Sarkin Kabba, Oba Solomon Owoniyi tare da CAN a Kabba/Bunu, sun dakatar da dukkan ayyukan coci sakamakon barazanar tsaro da hare-haren ‘yan bindiga.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari wani cocin ECWA a jihar Kogi. An kashe mutum daya yayin da aka sace mutane da dama. Gwamnatin Kogi ta yi Allah wadai da kai harin.
Sanata Natasha H Akpoti ta bayyana cewa ba ta da niyyar komawa jam’iyyar APC, duk da tayin da ta ce ana ci gaba da yi mata daga wasu a fadar shugaban kasa.
Gwamnonin jam'iyyar APC 6 sun shiga ganawa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. An ce ganawar an yi ta ne a sirrance kuma ba a yi wa 'yan jarida bayani ba.
Tsohon mai magana da yawun PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya yi murabus daga kasancewarsa mamba a jam'iyyar, ya ce lokaci ya yi da zai kama gabansa.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar da kara kan sanata mai wakiltar Kogi ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Natasha Akpoti.
An tabbatar da rasuwar marigayi Sanata Isa Abonyi Obaro, tsohon wakilin Okehi/Okene a tsohuwar jihar Kwara wanda ya rasu bayan hidima ga al’umma da kasa.
Shugaban Karamar Hukumar Omala a Kogi, Edibo Peter Mark, ya kafa dokar hana fita daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe saboda tsananin barazanar tsaro.
Jihar Kogi
Samu kari