Jihar Kano
Shugaban gidan rediyon kare hakkin bil'adama da ke Abuja, Ahmed Isa ya dakatar da shirin Brekete Family saboda bacin rai kan gurfanar da kananan yaran Arewa a kotu.
Lauya mai kare yan zanga zanga ya yi kira ga malamai da yan siyasa kan yaran zanga zanga. Lauyan ya ce wulaƙanta yaran zanga zanga cin mutuncin Arewa ne.
Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta samu kanta a cikin rikici. Wasu 'yan majalisar wakilai guda biyu na jam'iyyar sun fice daga tafiyar Kwankwasiyya.
Da yawa daga jihohin Najeriya na dogara ne da kason da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa duk wata a kasar domin gudanar da al'amuransu da biyan albashi.
Rahoton da muke samu ya bayyana yadda Farfesa Ibrahim Maqary ya ba da kudade domin a yiwa yaran da aka tsare a Abuja jinya kafin tabbatar da sun fito.
Hukumar gidajen yari ta yi magana kan rade-radin cewa ta tsare yara 72 da aka gurfanar da su a gaban kotu inda ya ce doka ba ta ba da wannan damar ba.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga jihar Kogi ta yi Allah wadai da tsare ƙananan yara babu ka'ida inda ta bukaci a yi bincike domin hukunta masu hannu a lamarin.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan yaran da aka gurfanar a gaban kotu. Gwamnan ya nuna cewa za su dauki matakin dawo da su zuwa Kano.
Tsohon dan takarar gwamna a Katsina kuma shugaban gidauniya Jino, Imran Jafaru Jino ya ce za su jagoranci neman diyyar asara da yan Arewa su ka tafka
Jihar Kano
Samu kari