Jihar Kano
Dan Kwankwasiyya, Kabiru Adamu Abdullahi, tsohon aminin Kwankwaso, ya fice daga NDC zuwa APC, yana mai cewa zai goyi bayan Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Shugaban Kwankwasiyya a karamar hukumar Nassarawa, Abdulaziz Gidanruwa, ya ziyarci Gwamna Abba Yusuf yayin da ake sa ran zai bar NDC zuwa APC gabanin 2027.
A labarin nan, Dan majalisar jiha mai neman takarar majalisar tarayya a Madobi/Kura/Garun Mallam ya ce duk da Kwankwaso mutumin kirki ne, dole yan takara su yi aiki.
Hukumar Jin Dadin Mahajjatan Kano ta sanya kuɗin kujerar Hajjin 2027 a N7m, tare da tsayar da 25 ga Agusta a matsayin ranar ƙarshe ta yin rajista ga maniyyata.
Dan majalisar tarayya, Leke Abejide ya shirya ƙaddamar da shirin tallafa wa mazauna Kano miliyan ɗaya domin ƙarfafa tattalin arziki da goyon bayan Tinubu
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 21 ga Satumba domin sauraron karar da ke neman hana Bola Tinubu tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Gwamnatin Kano ta umarci limamai su karyata bayanan ƙarya kan aurar da jama’a, yayin da ƙungiyar matasan masallatai ta goyi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Dan majalisar Tudun Wada, Sule Lawan Shuwaki, ya fice daga APC ya koma PDP, lamarin da ya sauya rabon kujerun jam’iyyun a Majalisar Dokokin Kano.
Jami’ar Northwest University Kano ta musanta wani bidiyo da ke zargin Sarki Sanusi II da gazawar karatu, tana mai cewa ikirarin ƙarya ne kuma ba shi da tushe
Jihar Kano
Samu kari