Jihar Kano
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta caccaki tsohon shugaban KASCO a jihar, Bala Inuwa kan zargin ta yi watsi da umarnin kotu kan kadarorinsa.
Gwamnatin Kano ta amince da murabus da daya daga cikin kwamishinoninta, Injiniya Muhammad Diggol ya yi, bayan sauya masa ma'aikata zuwa Ma’aikatar Kula da Ayyukan.
Gwamnan jihar Kano ya nada kwararru kan ayyukan gwamnati, ciki har da Ahmad Speaker da Sani Tofa. An shirya rantsar da su ranar 6 ga Janairu, 2025.
Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, na shekara guda saboda hotuna da bidiyo na batsa da suka tada hankali.
A yau Asabar 4 ga watan Janairun 2025 aka daura auren 'ya'yan shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas inda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarta.
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana nasarar damke wata matashiya, Shamsiyya Adamu da ta kware wajen satar wayoyin hannu tare da masu ba da gudunmawa.
NDLEA Kano ta kama mutane 1,345 da kwace 8.4kg na kwayoyi. Ta rushe sansanonin kwayoyi 20, ta gyara halin masu shaye shaye 101 da kuma hukunta 128.
Wani saurayi ya siya wa fitacciyar 'yar TikTok a Arewa, Maryam Sa'idu gida na N55m, ya ce ta daina zama a otel. Maryam ta ce ba za ta yi aure ba sai Tinubu ya sauka.
Abdullahi Tijjani Gwarzo wanda ya rike muƙamin tsohon Minista, ya yaba wa shugaba Bola Tinubu kan jagoranci da gyare-gyare don ci gaban Najeriya.
Jihar Kano
Samu kari