Jihar Kano
Yayin da ake zargin rigima tsakanin Sanata Rabi'u Kwankwaso da Abba Kabir, jigon jam'iyyar APC a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi tsokaci kan abubuwan da ke faruwa.
Kungiyar masu kafafen yada yada labarai ta Northern Broadcast Media Owners Association (NBMOA) maka tashar talabijin din Arewa24 da wasu guda bakwai a gaban kotu.
Mazauna Kano sun koka kan matsalar karancin takardun Naira a yan kwanakin nan, masu POS sun bayyana cewa ƴan kasuwa sun daina kai kuɗaɗensu bankuna.
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi bayani kan samuwar yan bangaren Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf a majalisa. Ya ce ba ruwansu da zancen Abba tsaya da kafarka.
Kungiyar likitoci ta kasa (NMA), reshen jihar Kano ta ba gwamnatin jihar wa'adin awanni 48 ta kori kwamishiniyar walwala da jin kai ta jihar, Hajiya Amina Abdullahi.
Shugaban gidan rediyon kare hakkin bil'adama da ke Abuja, Ahmed Isa ya dakatar da shirin Brekete Family saboda bacin rai kan gurfanar da kananan yaran Arewa a kotu.
Lauya mai kare yan zanga zanga ya yi kira ga malamai da yan siyasa kan yaran zanga zanga. Lauyan ya ce wulaƙanta yaran zanga zanga cin mutuncin Arewa ne.
Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta samu kanta a cikin rikici. Wasu 'yan majalisar wakilai guda biyu na jam'iyyar sun fice daga tafiyar Kwankwasiyya.
Da yawa daga jihohin Najeriya na dogara ne da kason da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa duk wata a kasar domin gudanar da al'amuransu da biyan albashi.
Jihar Kano
Samu kari