Jihar Kano
Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun samu bayanan sirri cewa yan garin Bichi na shirin wargaza bikin nadin hakimi a garin wanda shi ne ake zargin dalilin daukar mataki
Wasu rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa lamura sun koma yadda suke bayan janye jami'an tsaro a fadar Sarki Muhammadu Sanusi II a yau Asabar.
Dan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuwa kan yadda makiya ke neman kawowa mahaifinsa tsaiko inda ya ce babu mai hana abin da Allah ya ƙaddara.
An jibge jami'an tsaro a kofar masarautar Bichi. An fitar da sarakan da ke dakon isowar sabon hakimi. Gwamnati ta sanar da dage nada sabon hakimi a Bichi.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi martani yayin da tarin jami'an tsaro suka mamaye fadar Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu. Sarkin ya ce "Hakuri ba tsoro ba ne."
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya dira a Kano domin kai ziyara sashen kamfanoni da ke Challawa da kuma rukunin kamfanin Mamuda a jihar.
Kotu ta jingine dakatar da shugaban hukumar hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado da kotun ladabar da ma'aikata ta yi.
Sheikh Muyideen Bello ya rasu yana da shekaru 84. Fitaccen malami ne da ya yada addinin Musulunci, yana jan hankalin jama’a kan kyawawan dabi’u da gaskiya.
Sakataren gwamnatin jihar Kano ya bayyana cewa sun yi matuƙar mamaki da suka samu labarin jami'an tsaro sun hana shiga da fita a fadar sarkin Kano.
Jihar Kano
Samu kari