Jihar Kano
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nada sababbin mukamai, inda aka zabo da yawa daga cikinsu matasan 'yan siyasa, daga ciki har da Auwal Lawan Aramposu.
Jarumi a masana'antar Kannywood, Sadik Sani Sadik ya ce yana fim ne ba don koyar da tarbiyya ba, illa neman kuɗi kawai saboda tarbiyya daga gida ake samu.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa jami'an tsaro sun shirya bayar da tsaro, yayin da jama'a za su gudanar da bukukuwan hawan karamar sallah mai zuwa.
Sanata Barau Jibrin ya karɓi manyan ‘yan SDP da suka sauya sheka zuwa APC, yana mai cewa sun fahimci irin cigaban da jam’iyyar ke kawowa Najeriya.
Dan Majalisar Tarayya daga jihar Sokoto, Hon. Sani Yakubu ya dauki nauyin karatun wasu dalibai 21 a jami’a domin tallafa musu wajen samun ilimi mai inganci.
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta ba da umarnin kama tsohon Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari'a a mulkin Abdullahi Ganduje mai suna Barista M. A. Lawal.
Gwamna Abba Yusuf ya naɗa Ibrahim Adamu Kwamishinan Raya Gidaje na Kano, yana mai buƙatar ya tunkari matsalar gidaje, musamman ga ma’aikatan gwamnati.
Gwamnatin Kano ta bukaci ma’aikatan jihar da su tantance albashinsu na Maris, kafin ta fara biya, tana mai cewa za a biya kafin Sallah don su samu walwala.
Gwamnonin jihohin kasar nan sun fara neman a lallaba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a kan ya taka burki kan shirin biyan kananan hukumomi kudinsu kai tsaye.
Jihar Kano
Samu kari