Jihar Kano
Karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya taso Rabiu Musa Kwankwaso a gaba kan kalaman da ya yi dangane da dokar ta baci a Rivers.
Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukaci ‘yan adawa su daina sukar Shugaba Bola Tinubu inda ya ce su ba shi dama ya gyara kasa.
Sanata Barau Jibrin ya samu goyon bayan masu shirya shirin dogon zango na Dadinkowa a Abuja. Dalhatu Musa Dakata da aka fi sani da Nuhu Kansila ya jagorance su.
Jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Agbo Major ta bayyana cewa yarjejeniyarta da ƴan Kwankwasiyya ta kare bayan kammala zaben shugaban kasa na 2023.
Jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta gargadi gwamnatin Kano da cewa za ta iya jawo wa kanta dokar ta baci da irin furucin da ta yi a kan Hafsa Ganduje.
Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya yabi Baban Chinedu da ya fara wa'azin kalubalantar Kiristoci a Najeriya. Asadussunnah yana tare da Baban Chinedu.
Musa Ilyasu Kwankwaso, ya yi magantu kan sarautar Kano inda ya ce Sanusi Lamido Sanusi Sarkin gwamnati ne, Aminu Ado Bayero kuma na Sarkin al’umma.
Tsohon ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Kano, Hon. Adnan Mukhtar TudunWada ya soki ziyarar da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya kawo jihohin Arewa.
Alhaji Nasiru Ahali, attajiri kuma ɗaya daga cikin shuwagabannin masana’antu na farko a Kano, ya rasu yana da shekaru 108, inda za a yi jana’izarsa a Kurna Asabe.
Jihar Kano
Samu kari