Jihar Kano
Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya kauracewa ambaton Aminu Bayero da “Sarkin Kano” a Calabar, lamarin da ya jawo cece-kuce kan rikicin masarautar.
Wasu daga cikin mazauna Kano sun bayyana fatan sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki za su ajiye batun gudanar da hawan Sallah don kare rayukan jama'a.
Tsohon ministan wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce za a iya amfani da rikicin sarautar Kano wajen sanya dokar ta baci a Kano kamar yadda aka yi a Rivers
Abba Kabir Yusuf ya karbi murabus din kwaishinan tsaron cikin gida na jihar Kano Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya). Ya yi murabus ne ranar Talata.
Rundunar ƴan sandan Kano ta yi magana kan yadda ake shirin gudanar da hawan Sallah karama a jihar, inda ta ce ta samu labarin sarakuna biyu na shirin hawa.
Gwamnatin Kano da bangaren Aminu Ado Bayero na jiran Kotun Koli ta yanke hukunci kan halaccin nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.
Kungiyar Amnesty International ta bukaci a saki ƴan jarida biyu da aka tsare a Kano, tana mai cewa hakan cin zarafi ne da tauye ƴancin fadar albarkacin baki.
Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara kasuwar Dakata da aka yi gobara, ya ziyarci Sheikh Uwaisu Limanci, Asibitin yara da gidan gajiyayyu.
Gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Abba Kabr Yusuf ta bayyana takaicin yadda wasu ke kokarin hadda husuma jihar, musamman a kan batun sarauta a jihar.
Jihar Kano
Samu kari