Jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan N15.6bn ga tsoffin kansiloli 3,000 da suka yi aiki a mulkin Ganduje domin cika alkawarin biyansu hakkokinsu.
Wata kungiyar matasa ta daliban APC a jihar Kano ta ce komawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba za ta amfani jam’iyyar ba, saboda rashin tasirinsa yanzu.
Abdullahi Ganduje ya jagoranci kaddamar da masallacin Juma’a da ministar Abuja, Dr. Mariya ta gina a Bunkure, inda ya yabawa kokarinta wajen ci gaban addini.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya sauya ra'ayi kan tsarin karba-karba a Najeriya, yana mai cewa cancanta, ba yankin dan takara ba.
Dan majalisa mai wakiltar Bichi a majalisar wakilai, Hon Abubakar Kabir Bichi zai dauki nauyin dalibai mata 'yan asalin karamar hukumar domin karo karatu.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai ziyara ta musamman ga Muhammadu Sanusi II a fadarsa da ke birnin Kano inda ya ce jihar na da muhimmanci a siyasa.
Tsohon Sakataren gwamnatin Kano, Baffa Bichi ya zargi NNPP da fifita kansu a maimakon talakawa, ya ce shakar mutuwa ce ta sa suka fice daga jam’iyyar.
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi sabon nadi a masarautarsa. Sarkin ya nada yayansa Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano.
Yayin da Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi hawan Babban Daki, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya halarci taron sarakunan Arewa da aka gudanar a birnin Kaduna.
Jihar Kano
Samu kari