Jihar Kano
Kungiyar lauyoyin Kano ta shigar da korafi gaban shugaba Bola Tinubu da NSA, Nuhu Ribadu game da shirin Abdullahi Ganduje na kafa sabuwar Hisbah a Kano.
Kano ta shiga gaban sauran jihohin Najeriya bayan kungiyar gwamnoni ta yaba mata kan ware fiye da N400bn—kashi 30% na kasafin 2026—don inganta ilimi da gyare-gyare.
Tsohon kwamishinan Kano, Muaz Magaji ya soki shirin kasa sabuwar Hisbah da Abdullahi Ganduje ke shirin yi a Kano. Ya ce Ganduje zai kawo fitina a Kano da Arewa.
Kungiyoyin matasan Arewa a jihar Kano sun soki yunkurin kafa sabuwar Hisbah da za ta dauki jami’an da aka sallama, suna cewa hakan barazana ne ga doka.
Wata kungiya ta yi Allah wadai da shirin Abdullahi Ganduje da mutanensa kan neman kafa sabuwar Hisbah a Kano. Kungiyar ta ce lamarin zai jawo fitina jihar Kano.
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya ce lokaci bai yi ba da za a fara tallata dan takarar gwamna karkashin APC a Kano bayan fara tallata Barau.
Jam'iyyar hamayya ta NNPP ta bayyana ra'ayinta a kan yunkurin hadewa ko shiga wata hadaka da jam'iyya mai mulki ta APC gabanin zaben 2027 da ke tafe.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun sake kai hari a jihar Kano. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da wani dattijo tare da raunata dansa a harin da suka kai.
Shugaban Majalisar Shari'a ta Najeriya, Dr. Bashir Aliyu ya ce mutane na kara natsuwa da harkokin bankin musulunci ne saboda yadda yake da adalci da kaucewa haram.
Jihar Kano
Samu kari