Malamin addinin Musulunci
Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ba ta da shirin rusa babban masallacin Ilesa saboda aikin titin hanya.
Shugaban kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya bukaci a soke dokar da ta ba gwamnatin jihar Sokoto damar sauke Sarkin Musulmi daga kujera.
Sarkin Ogbomoso da ke jihar Oyo, Oba Afolabi Ghandi ya kalubalanci limamin masallacin Juma'a kan saba ka'idar da suka yi kafin nada shi mukami a jihar.
Sheikh Isa Ali Pantami ya yi alkawarin tallafawa wani matashi mai suna Umar Ibrahim Umar domin ya fara sana'ar POS. Matashin ne ya fara neman taimako.
Malamin Musulunci, Sheikh Muhydeen Bello ya soki 'yan siyasar Najeriya kan amfani da lokacinsu wurin taimakon al'umma inda ya bukaci su hada kai domin kawo ci gaba.
Kungiyar mata masu tafsiri a jihar Kano ta ziyarci fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II domin nuna goyon bayansu gare shi bayan dawowa kujerar sarauta.
Kasar Saudiyya ta amince da nadin Sheikh Abdulwahab Al-Shaibi a matsayin sabon mai rike makullin ɗakin Ka'aba. Shi ne na 110 a tarihin masu rike makullin
Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya tsoma baki kan dambarwar sarautar Kano inda shawarce su kan yin abu domin Allah.
Saleh Al-Shaibi ne na 109 cikin wadanda suka rike makullin Ka'aba tun daga kan sahabi Usman Bin Dalha. Yan kabilar Shaibah ne ke rike da makullin a tsawon tarihi.
Malamin addinin Musulunci
Samu kari