Kungiyar Shi'a
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, Bennett Igweh, ya sha alwashin cafke ‘yan Shi'an da ke da alhakin kisan gillar da aka yi wa jami’ansa.
An rasa rayukan mutum uku ciki har da na jami'an 'yan sanda mutum biyu yayin da 'yan kungiyar IMN mabiya Shi'a suka fito kan tituna a birnin tarayya Abuja.
Bayan fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Najeriya, an samu mutuwar mutane 14 a jihohin Kaduna, Borno, Niger da Kebbi dukkansu a Arewacin Najeriya.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta dauka mataki kan duk wanda ya fito tattakin ranar Ashura a jihar. Ta ce hakan na kawo tashin hankali.
Biyo bayan mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi a hadarin jirgin sama, mataimakinsa, Muhammad Mokhber zai dawo sabon shugaban kasa kafin sabon zabe.
Ana ci gaba da bayyana rahotanni kan faduwar jirgin sama mai saukar ungulu na shugaban kasar Iran a ranar Lahadi. Ya zuwa yanzu an ce babu mutuwa ko rauni.
Kasa da kwanaki 10 bayan kisan 'yan Shi'a guda bakwai a Kaduna, shugaban Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya karyata cewa suna shirin daukar fansa.
Kungiyar IMN ta yi ikirarin cewa jami'an tsaro sun kashe ƴan shi'a huɗu a arangamar da ta faru a Kaduna ranar Jumu'a, kakakin ƴan sanda ya musanta.
Dakarun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun yi arangama da ƴan shi'a a ranar Jumu'a ta karshe a watan Ramadan, ranar da suke kira da ranae Guds.
Kungiyar Shi'a
Samu kari