Addinin Musulunci da Kiristanci
Wani malamin addini a jihar Filato ya jagoranci matasa zuwa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Filato. Dakta Isa El-Buba ya ce wahalar rayuwa ta yi yawa.
Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN ta fadi matsayarta kan zanga-zanga bayan malaman Musulunci inda ta yi gargadi kan fita zanga-zanga a fadin kasar.
Cocin ECWA a jihar Filato ya bukaci matasa da ke cocin su nisanci fita zanga zangar tsadar rayuwa da ake shirin gudanarwa saboda kaucewa ta da tarzoma a kasa.
Kungiyar kare hakkin musulmi ta kasa (MURIC) ta yi gargadi a kan wani sabon fim da ke nuna mata a cikin hijabi su na fashi, inda kungiyar ta ce hakan bai dace ba.
Shugaba Bola Tinubu ya roƙi matasan Najeriya da kada su fito zanga-zangar da suke shiryawa. Ya bayyana irin tagomashin da ya gwangwaje 'yan Najeriya da shi.
Bishof a cocin Anglican Diocese da ke Owo a jihar Ondo, Rabaran Stephen Fagbemi ya bi jerin malaman addini da su ka bawa shugaba Tinubu shawara ka halin da ake ciki.
Gwamnatin jihar Lagos ta shirya kakaba karbar haraji kan masu ajiye ababan hawa a wuraren ibada da sauran hanyoyi wanda ake sa ran zai fara aiki a watan Oktoba.
Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya tura sakon godiya ga al'umma kan addu'o'insu inda ya ce tabbas addu'a ce ta yi tasiri wurin sakin mahaifyarsa.
Wani fusataccen Fasto a jihar Enugu mai suna Linus Okwu ya zane mambobin cocinsa saboda sun ki share harabar wurin ibadar yadda ya umarce su gaba daya.
Addinin Musulunci da Kiristanci
Samu kari