Addinin Musulunci da Kiristanci
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar su guji bambancin addini da kabilanci, yana mai cewa ƙauna da zaman tare su ne ginshiƙan ci gaba.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wani kisan kiyasin addini da ake yi a Najeriya, ya ce duk irin jita-jitar da ake yadawa karya ce don ta da hankula.
Tsohon hadimin shugaban kasa a Najeriya, Reno Omokri ya karyata zargin wani mai gabatar da shirye-shirye na Amurka, Bill Maher cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin kisan kiyashi a Najeriya, ta ce ’yan ta’adda suna kai hari ga Musulmi da Kiristoci ba tare da bambancin addini ba.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa an yi rashin babban Fasto a jihar Benue, Simon Agu Mashika da aka ce ya fi kowa dadewa yana wa'azi a jihar.
Kungiyar matasan Kiristoci ta yi fatali da dokar haramta wa'azi a jihar Niger tana cewa kwata-kwata ba ta dace ba, tana nuna wariya, kuma zalunci ce.
Rundunar yan sanda da ke Lagos ta ce ta wanke babban Faston House on the Rock, Fasto Paul Adefarasin, bayan bidiyon bindiga ya bazu wanda ya tayar da kura.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin dakile talauci gaba daya a fadin Najeriya inda ta ce za ta bi duk hanyar da ta dace domin kawo sauyi a kasa.
Gwamna Umar Bago ya ce dole malamai da limamai a jihar Neja su mika hudubarsu domin tantancewa kafin su yi, abin da ya haifar da martani daga malamai da CAN.
Addinin Musulunci da Kiristanci
Samu kari