
Addinin Musulunci da Kiristanci







Gwamna Soludo ya haramta wa’azi a kasuwannin jihar Anambra, yana mai cewa yana haddasa hayaniya. Shugabannin addini sun ce hakan cin zarafin ‘yancin addini ne.

Gwamnatin jihar Anambra ta haramta wa’azi da lasifika musamman a kasuwanni tana mai cewa hayaniya na hana mutane sukuni inda ta ce babu dole a yin addini.

Yayin da aka shiga watan azumin Ramadan akwai wasu hanyoyi da mutum zai bi domin sauke Alkur'ani mai girma a cikin kwanaki 30 kacal a watan azumi.

Shugaban CAN, Rabaran Daniel Okoh ya yi buda baki da Musulmai a masallaci inda ya bukaci zaman lafiya tsakanin addinai yayin ziyararsa a masallacin Al-Habibiyya.

Yayin da ake maganganu kan rufe makarantu a Ramadan, Majalisar shari’ar Musulunci ta goyi bayan matakin a Ramadan, tana cewa hakan zai taimaka wa dalibai.

Kungiyar CAN ta gargadi wasu gwamnonin Arewacin Najeriya guda hudu kan rufe makarantu saboda samun sauki a azumin watan Ramdan da ake ciki a yanzu.

Rabaran Matthew Kukah ya ce mutane 12,000 sun mutu a Arewa maso Yamma cikin shekaru 10, sakamakon hare-haren 'yan ta'adda. AAn kawo hanyoyin dakile rikicin.

Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokir ya bayyana cewa bai ga abin da zai jawo maganganu a kan hutun Ramadan da wasu jihohin Arewa su ka bayar ba.

Kungiyar Kiristoci a Najeriya, CAN ta bukaci jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi su janye matakin rufe makarantu na makonni biyar don azumin Ramadan.
Addinin Musulunci da Kiristanci
Samu kari