INEC
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce a kan gaba bayan da hukumar zabe ta INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 13 na jihar Edo a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Godwin Obaseki ya gaza ba jam'iyyar PDP nasara a karamar hukumarsa ta Oredo a zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar.
Ba a gama tattara sakamakon zaben jihar Edo ba, magoya bayan PDP sun durfafi ofishin INEC da ake tattara sakamakon zaben domin gudanar da zanga-zanga.
Rahotanni sun bayyana cewa Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP Asue Ighodalo ya yi nasara a karamar hukumarsa ta Esan ta Kudu maso Gabas.
Nan da 'yan awanni za a san wanene zai zama sabon gwamna a jihar Edo inda ake zabe. INEC ta yi maganar soma tattara sakamako, a san wanda ya lashe zaben Edo.
Rahotanni daga cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke da zama a birnin Benin ta sanar da cewa PDP ta samu kuri'u 5,311 a Ovia ta Arewa maso Gabas.
Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Edo ta samu nasarar lashe karamar hukumar Uhunmwonde da kuri'u 9339 bayan da hukumar INEC ta ci gaba da sanar da sakamako.
Rahotanni daga cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke Benin City na nuni da cewa jam'iyyar APC ta lashe zabe a karamar hukumar Esan ta Yamma.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.
INEC
Samu kari