Jihar Imo
Gwamnatin Imo ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na ₦104,000 ga ma’aikata, matakin da ya sanya ta kan gaba a Najeriya wajen inganta walwalar ma’aikata.
Jam’iyyar ADC ta shiga jimami bayan mutuwar mataimakin sakataren hulda da jama'a na Imo, Hon. Ugochimereze Asuzu, wanda aka bayyana a matsayin babban jigon Inyamurai
Shugaba Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya yi kokarin rubuta littafi a baya amma bai samu nasara ba. Ya fadi haka ne yayin kaddamar da littafi a Imo.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wani kisan kiyasin addini da ake yi a Najeriya, ya ce duk irin jita-jitar da ake yadawa karya ce don ta da hankula.
Gwamnatin Imo ta yi alƙawarin ceto tsohon ɗan majalisar jihar, Ngozi Ogbu, wanda wasu mayaka masu fafutukar kafa Biyafara suka sace shi, tare barazanar kashe shi.
A labarin nan, za a ji cewa cocin katolika ta karyata jita-jitar cewa Nasir El-Rufa'i ya gudanar da jawabi a wani taronta da addini da aka saba yi duk shekara.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana takaicin yadda ake samun karuwar talauci a Najeriya tun bayan 1960.
Daruruwan masu zanga-zanga sun yi wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ihu a Owerri da ke jihar Imo bayan wata ziyara da ya kai da Nasir El-Rufai.
Gwamnoni da dama sun haura dokar mafi karancin albashin Najeriya watau N70,000, jihar Imo ce a sahun gaba bayan Uzodinma ya yi kari zuwa N104,000.
Jihar Imo
Samu kari