
Ibadan







Rahotanni sun tabbatar da cewa an sanar da rasuwar Sarkin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Haruna Maiyasin bayan ya shafe shekaru da dama a sarauta.

Yan kwadago sun fita zanga zangar nuna adawa da korar ma'aikata sama da 3000 a kamfanin rarraba wuta na Ibadan watau IBEDC, sun gabatar da buƙatu 7.

Bayan shafe tsawon lokaci ana rigima kan kujerar sarauta, kotun daukaka kara a Ibadan ta yi zama kan rigimar sarauta a jihar Oyo kan kujerar Soun na Ogbomoso.

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayyana cewa yana da burin shiga soja, amma hakan bai samu ba saboda wasu dalilai inda ya yaba wa tasirin marigayi yayansa.

Bayan rasuwar yayan Gwamna Seyi Makinde ya rasu, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jajanta masa kan babban rashi da ya yi a yau Juma'a.

Yayan gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Injiniya Sunday Makinde ya rasu da daren ranar Juma'a a gidanda da ke Ibadan, iyalai da ƴan uwa sun fara jimami.

Hukumar kwana-kwana ta tabbatar da faɗuwar wata fankar man fetur a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta ce direba ya rasa rayuwansa amma an ceto yaron mota.

Masu zaben sarki a jihar Oyo sun gindaya wa'adin kwanaki 30 ga Gwamna Seyi Makinde ya soke naɗin sabon Alaafin, sun ce ba shi da hurumi a wannan al'amarin.

Gwamna Seyi Makinde ya gargadi masu neman ta da rigima bayan an zabi sabon Alaafin na Oyo, Oba Akeem Abimbola Owoade, ta hanyar gaskiya da adalci.
Ibadan
Samu kari