Yan jihohi masu arzikin man fetur
Mutanen yankin Neja Delta sun caccaki Bola Tinubu kan zargin rusa musu ma'aikata. Wasu daga cikinsu sun yi madalla da rusa ma'aikatar da Bola Tinubu ya yi.
Kamfanonin NNPCL da Chevron sun yi nasarar hakar wata rijiyar mai da aka samu alheri a Yammacin Neja Delta da ke Kudancin kasar domin inganta Najeriya.
Yayin da aka shiga jimamin rasa rayuka sama da 107 a Jigawa bayan fashewar tankar mai, wata tankar makare da fetur ta fadi a jihar Ogun, an tafka asara.
Masu kasuwancin man fetur za su zauna da matatar Dangote domin tattauna farashin da matatar za ta sayar masu da fetur. Za a yi zaman a makon nan.
Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ya roki gwamnatin tarayya da ta dawo da farashin man fetur kamar yadda yake a watan Yunin 2023, kusan N450 kan kowace lita.
Kungiyar IPMAN ta ce ‘yan kungiyarta sun biya kudin fetur ne tun kafin karin farashin man da aka yi a baya-bayan nan. Ta nemi NNPCL ya dawo mata da kudinta.
Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harris, ya ce lokaci ya yi da Dangote zai ba da damar tattaunawa kai tsaye ga dillalai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar mai.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) na kasa, Abubakar Garima ya zargi kamfanin main a NNPCL da yi masa shigo-shigo ba zurfi kan farashin fetur.
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa yadda yan kasar nan su ka ji labari, ita ma haka ta tsinci batun karin farashin litar fetur.
Yan jihohi masu arzikin man fetur
Samu kari