Rikcin makiyaya a Najeriya
Rundunar 'yan sanda jihar Bauchi ta kama mutum shida a wani fada da aka gwabza tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Zaki. An kashe mutum daya.
Wasu makiyaya sun koka game da harin da aka kai musu a wasu yankunan jihar Benue. Sun ce an kashe musu shanu 259 jerin hare haren da aka kai musu a Benue.
Kungiyar MACBAN ta roƙi Shugaba Donald Trump da Majalisar Dokokin Amurka su cire sunanta daga duk wani jerin sunaye da ke danganta ta da ta’addanci a Najeriya.
Gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da sarakunan gargajiya kan manoma da makiyaya a karamar hukumar Funakaye. Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane.
Wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Benue ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3. Har yanzu ana neman mutum daya da ba a same shi ba.
Rikicin manoma da makiyaya ya yi kamari a karamar hukumar Darazo da ke jihar Bauchi ya jawo daina zuwa gona. Manoma sun bukaci gwamna ya dauki mataki.
Ana fargabar makiyaya sun kashe mutane 9 ciki har da dan sanda a Benue, yayin da matsalar tituna ke hana jami’an tsaro isa cikin gaggawa domin ceto rayuka.
Sabon rikici ya barke a jihar Filato tsakanin makiyaya 'yan kabilar Fulani da wasu mazauna karamar hukumar Bokkos. An kashe wata mata tare da kona gidaje.
'Yan ta'adda da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kone gidaje 100 a yankin Bandawa Gwenzu na karamar hukumar Karim Lamido a Taraba. Mutum 1 ya mutu.
Rikcin makiyaya a Najeriya
Samu kari