Hare-haren makiyaya a Najeriya
Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga munanan hare-haren da yan bindiga suka kai a yankin Bokkos sun ba da labarin yadda lamarin ya faru ba zato ba tsammani.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa ba rikicin manoma da makiyaya ne ke jawo asarar rayuka a jiharsa ba, ya ce akwai masu ɗaukar nauyi a gefe.
Hare-haren da aka kai kan garuruwa biyar a Bokkos sun yi sanadiyyar mutuwar mutum goma. BCDC ta yi kira ga jama’a su kare kansu daga barazanar ‘yan ta’adda.
Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta kama mutum 15 bayan Fulani makiyaya sun gwabza fada mai muni da Hausawa. An samu gawar wani matashi cikin jini.
Tsohon ɗan majalisar karamar hukuma a jihar Osun ya rasa ransa a wani sabon azababben faɗa da ya kaure tsakanin mazauna kauyuka 2, an tafka asara.
Akalla mutum 1 aka tabbatar ya mutu da faɗa ya ɓarke tsakanin mutanen gari da makiyaya, waɗanda suka suka yi ƙoƙarin shayar da shanunsu ruwan da mutane ke sha.
rundunar 'yan sanda ta kama wani mutum da ya rika yada takarda cewa Fulani makiyaya za su kai hari Imo. Ya ce Allah ya yi wahayi ne ga malamar coci.
Jihar Jigawa da ke fama da matsanancin rikicin manoma da makiyaya ta fara kokarin hada kan bangarorin biyu domin tabbatar da an daina zubar da jinin jama'a.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kafa ma'aikatar kiwo domin magance matsala da rikicin manoma da makiyaya da bunkasa tattalin jihar a Itas Gadau.
Hare-haren makiyaya a Najeriya
Samu kari