Hajjin Bana
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bukaci majalisar tarayya da ta binciki tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta ba hukumar NAHCON domin hajjin bana.
Kungiyar 'yan jarida ta IHR ta jinjinawa hukumar jin dadin alhazai a jihar Kaduna bayan dawowa mahajjata kudi kimanin $50 saboda sauki da aka samu kan hadaya.
Jirgin farko da ya kwaso alhazan Najeriya daga Saudiya ya Iso gida. Kashi na farko na alhazai 410 daga jihar Kebbi da suka yi aikin Hajjin bana sun dawo gida.
Rahotanni sun bayyana cewa Ƙasar Masar ta rasa alhazai 600 waɗanda suka rasu sakamakon tsananin zafin da aka yi fama da shi a aikin hajjin bana a Saudiyya.
Alhaji daga jihar Jigawa ya ƙara ɗaga kimar Najeriya yayin da ya mayar da jakar kuɗin da ya tsinta a Masallacin Annabi SAW a Madinah, ya yi cigiya bai ga mai ita ba.
Hukumar kula da alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta mayarwa wadanda su ka biya kudin aikin hajji ta hukumar su 700 kudin ragon layyarsu.
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta hana mahajjata dauko ruwan ZamZam daga Saudiyya yayin da suke dawowa gida Najeriya. Hukumar ta ce za a ba su idan sun iso.
Sama da musulmi 900 ne su ka kwanta dama yayin aikin hajjin bana, yayin da mutane da yawa ke neman ‘yan uwansu da aka nema aka rasa a kasa mai tsarki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani Alhaji da ya fito daga jihar Plateau ya riga mu gidan gaskiya a Saudiyya. Alhajin ya rasu ne bayan ya yi jinya a asibiti.
Hajjin Bana
Samu kari