
Hajjin Bana







Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar kasa (EFCC), sun kai samame a hedkwatar hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) da ke Abuja.

EFCC ta gurfanar da wani Mustapha Mohammed kan damfarar alhazai Naira miliyan 144 da sunan kai su Umrah. Kotun Gombe ta umarci a tsare shi a gidan yari.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ba da shawara kan hanyar gudanar da aikin Hajji. Gwamna Radda ya bukaci a rage yawan kwanakin da Alhazai ke yi.

Hukumar kula da alhazai ta jihar Kwara ta ce ranar ƙarshe ta biyan kuɗin Hajjin 2025 ita ce Janairu 31, 2025. An nemi alhazai su gabatar da fasfo kafin Fabrairu 25.

Hukumar NAHCON ta ce maniyyata aikin hajjin 2025 za su samu tallafin $500. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi ya fadi matsalolin da aka samu a shekarar 2024.

Hukumar jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON), ta sanya lokacin da maniyyata za su kammala biyan kudaden Hajji na shekarar 2025. NAHCON ta ce ba za ta yi kari ba.

NAHCON ta amince da Naira miliyan 8.7 a matsayin kudin aikin Hajjin 2025 ga maniyyatan Kudu, sai Naira miliyan 8.3 ga 'yan Arewa maso Gabas. Ta yi karin bayani.

NAHCON ta sanar da cewa gwamnati ta zabi jirage 4 don jigilar alhazai a aikin Hajjin 2025. Haka zalika, hukumar ta cimma yarjejeniya da kasar Saudiyya.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roki alfarma wajen shugaba Bola Ahmed Tinubu domin rage kudin aikin hajjin 2025 saboda matsin tattalin arziki da ake fuskanta
Hajjin Bana
Samu kari