Gwamnan Jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Lawal Jobe. Gwamnan ya tafi hutun wata daya.
Kungiyar dattawan Katsina ta KSEF ta bayyana damuwa a kan yadda gwamnati ta yi rikon sakainar kashi da batun tsaro da kawo kudurin halasta auren jinsi da dangoginsa.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ba da hutu a jihar domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH. Gwamnan ya ce ba aiki a ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya kulla yarjejeniya da hukumar SMEDAN domin ba kananun 'yan kasuwar Katsina tallafin N1bn.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bukaci al'ummar jihar Katsina da su koma ga Allah domin samun mafita kan matsalar rashin tsaro.
An jero ayyukan gwamnan Katsina daga hawansa mulki. Hadimin gwamnan na jihar Katsina ya tallata mai girma Dikko Radda, ya ce ya yi ayyukan ne a cikin shekararsa daya
Yan bindiga sun turo sakon gargaɗi da barazana kwanaki kalilan bayan sun shiga garin Maidabino da ke karamar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina, sun sace mutum 50.
Yan ta'adda sun yiwa ayarin jami'an tsaro kwantan ɓauna a yankin ƙaramar hukumar Jibia a jihar Katsina, sun hallaka ƴan sanda biyar ranar Lahadi.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta bayyana cewa jami'anta sun samu nasarar kama mutum buyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar Dauda Rarara.
Gwamnan Jihar Katsina
Samu kari