Gwamnan Jihar Katsina
Gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta nanata cewa ba za ta nemi zaman sulhu da kowane ɗan bindiga ba amma za ta karɓi duk wanda ya tuba ya miƙa wiya.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kai kan ma'aikatan lafiya a babban asibitin Kankara.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa watau EFCC ta cafke jami'an gwamnatin Katsina 5 bisa zargin karkatar da kimanin N.1.3bn.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindiga sun yi wa jami'an askarawa da ƴan banga kwantan ɓauna a jihar Katsina, majiyoyi sun ce an kashe rayukan mutane akalla 21.
Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 kamar yadda aka yi alƙawari.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyara a asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina. Gwamnan ya duba marasa lafiya tare da ba su tallafin kudi.
Gwamnati ta aika N748,320 ga wata malama a jihar Katsina bisa kuskure. Kudin na daga cikin wanda ake amfani da shi don ciyar da dalibai, amma ta mayar da kudin.
Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da kasafin kudin shekarar 2025 da Gwamna Dikko Umaru Radda ya gabatar mata. Majalisar ta yi wa kasafin gyara.
Gwamna Dikko Umaru Radda zai kaddamar da raba tallafin Naira biliyan 3.9 domin farfado da tallafi. Manoma, yan kasuwa da yankuna za su samu tallafin.
Gwamnan Jihar Katsina
Samu kari