Gwagwalada Abuja
Wani ginin bene ya rufto a birnin tarayya Abuja a yayin da ake tsaka da tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a daren ranar Laraba. Mutane da dama sun rasu.
Kwana biyu bayan kama aiki a matsayin ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana tsare-tsaren da hukumar babban birnin tarayya ke yi don farfado da layin dogo.
Idan za ayi rusau a Abuja, binciken FCTA ya nuna gidaje 6, 000 ake magana. Abin zai taba Gishiri, Gwagwalape, Idu, Jabi, Kado, Karshi, Karu, Kubwa, da Lokogoma.
Bwala, hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya gargaɗi sabon ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan yin rusau.
Sabon ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tada hankalin jama’a da ya fadi manufofinsa, zai fatataki ‘yan kasuwa da masu acaba da keke napep.
Fadar shugaban kasa ta sanar da ayyukan da aka bai wa zababbun ministoci, kuma ga mamakin mutane da dama Nyesom Wike aka bai wa ministan babban birnin tarayya.
Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wata motar tirela mai ɗebo yashi a birnin tarayya Abuja. Burkin motar tirelar ne ya ƙwace inda ta yi kan wasu motocin.
Rahotanni daga babban birnin tarayya sun nuna cewa wani ginin Bene mai hawa 4 da ba'a kammala ba ya kife kan mutanen da ke aiki a wurin, jami'ai sun kai ɗauki.
Mazauna rukunin gidajen Trademore a birnin tarayya Abuja, sun barke da zanga-zanga kan shirin FCTA na rushe anguwar da suke zaune saboda hadarin ambaliya .
Gwagwalada Abuja
Samu kari