Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Ministan birnin Abuja, Nyesom Wike murnar cika shekaru 58, yana yabonsa kan jajircewa da hidimar jama’a a rayuwarsa.
Kotu a Abuja ta umarci a tsare tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, a Kuje kan tuhumar rashawa da almundahana. Za a saurari bukatar belinsa a ranar Litinin.
Shugaban hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi ya bada umarnin sakin mutane uku da aka kama bisa zargin ta’addanci, bayan binciken hukumar ya tabbatar da ba su da laifi.
Kotun Koli ta rusa afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga Maryam Sanda, ta tabbatar da hukuncin kisa da kotu ta yi mata kan kashe mijinta da ta yi.
Kungiyar kwadagon NLC za ta yi zanga zanga a ranar 17 ga Disambar 2025 a dukkan jihohin Najeriya da Abuja. Za a yi zanga zangar ne saboda sace dalibai a jihohi.
Hukumar NMDPRA ta bayyana cewa amfani da fetur ya ragu zuwa lita miliyan 52.9 a rana a Nuwamba, raguwar da ta fito daga lita miliyan 56.7 da aka sha a Oktobar 2025.
Ministan Tsaro, Christopher Musa ya yaba da saurin daukar matakin sojojin Najeriya wurin dakile juyin mulkin Benin da aka yi yunkurin yi a karshen mako.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce EFCC ta tsare shi ba tare da bayyana dalili ba bayan soke belinsa duk da cewa ya cika sharuddan da aka gindaya masa.
Majiyoyi sun ce zazzafar muhawara ta kaure tsakanin Sanata Ali Ndume da Adams Oshiomhole yayin tantance sababbin jakadu a Majalisar Dattawa a Abuja.
Abuja
Samu kari