Guaranty Trust Bank - Gtbank
Daya daga shaidun hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annti (EFCC) ta bayyana yadda tsohon gwamnan bankin CBN ya boye kudi a asusun matarsa.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar hukunta duk wani bankin ajiyar kudi da aka kama yana kin karbar lalatattun takardun Naira daga abokan huldarsa.
Hukumar da ke kula da kudin masu ajiya a bankuna (NDIC) ta sanya bankin Heritage da sauran rassansa a sassan kasar nan a kasuwa a matsayinta Na mai sa ido.
Hukumar kare bayanan ‘yan kasa (NDPC) ta ce ta na binciken akalla kamfanoni, makarantu, kamfanonin inshora, cibiyoyin kasuwanci 1000 saboda shiga bayanan jama'a.
Babban dan kasuwa kuma attajiri a Najeriya, Femi Otedola, ya zargi bankin Zenith na Jim Ovia da yin amfani da asusun kamfaninsa ta hanyar da ba ta dace ba.
Rahotanni sun bayyana cewa asusun ajiyar kudin Najeriya na kasar wajen ya ragu sosai a cikin mako 10 da suka gabata, kamar yadda alkaluman CBN ya nuna.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata rahotannin da ke yawo a yanar gizo cewa zai soke lasisin bankunan Unity, Polaris, da Keystone. CBN ya yi karin haske.
Rahotanni sun bayyana an kwashi 'yan kallo a wani bankin Polaris da ke jihar Legas bayan da kungiyar kwadago ta NLC ta dura bankin tare da fatattakar jama'a.
Babban bankin Najeriya CBN ya ce ya kwace lasisin bankin Heritage Plc. Babban bankin ya ce matakin ya biyo bayan gazawar bankin Heritage na inganta harkokin kudi.
Guaranty Trust Bank - Gtbank
Samu kari