Jihar Gombe
Dan takarar PDP a Gombe, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana yadda zai magance kalubalen da jihar ke fuskanta. Ya ce yana da karfin gwiwar zai lashe zaben.
Ce-ce-ku-ce kan matsayin farfesa na Isa Ali Pantami ya jawo damuwa, yayin da aka bukaci masu zaɓen Gombe su binciki tarihin ‘yan takara game da 2027.
Shugaban matasan PDP na Jihar Gombe, Jamilu Ali Kalshingi, ya yi murabus daga mukaminsa da jam’iyyar, yana mai cewa ya ɗauki sabon alkibla ta siyasa.
Jam'iyyar SDP ta sanar da hukumar INEC shirin gudanar da sabon zaben fidda gwani a Gombe da Nasarawa domin maye gurbin ’yan takarar da suka janye.
Tsohon minista Isa Ali Pantami ya sami kashi 84% na kuri'u sama da 58,000 a zabukan gwaje-gwaje na yan gizo kan zaben gwamnan jihar Gombe na 2027.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Sarkin Bolari, Alhaji Ahmad Abubakar, rasuwa cikin daren nan bayan fama da rashin lafiya a birnin Gombe.
Shugaban jam'iyyar LP na Gombe, Usman Kalala, ya yi murabus ya koma PDP tare da Shehu Durbi da magoya bayansu, yana mai goyon bayan takarar Pantami.
Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala ya soki Atiku Abubakar bayan ya ce zai dawo da tallafin man fetur, ya ce ba shi ne ɗan takarar ADC ba a zaben 2027.
Sanata Danjuma Goje ya sake tabbatar da cewa yana cikin jam'iyyar APC, yana mai cewa ba zai sauya jam’iyya domin neman kujerar Majalisar Dattawa ba.
Jihar Gombe
Samu kari