
Fulani Makiyaya







‘Yan bindiga sun sace Wakilin Fulani da mutane 37 a Janjala, Kaduna, sun kwashe shanu, kuma har yanzu babu karin bayani daga ‘yan sanda kan matakin da za a dauka.

rundunar 'yan sanda ta kama wani mutum da ya rika yada takarda cewa Fulani makiyaya za su kai hari Imo. Ya ce Allah ya yi wahayi ne ga malamar coci.

Jihar Jigawa da ke fama da matsanancin rikicin manoma da makiyaya ta fara kokarin hada kan bangarorin biyu domin tabbatar da an daina zubar da jinin jama'a.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan yadda ake bata sunan al'ummar Fulani a kasar nan. Ya bayyana cewa ko kadan bai kamata ana yi musu hakan ba.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kafa ma'aikatar kiwo domin magance matsala da rikicin manoma da makiyaya da bunkasa tattalin jihar a Itas Gadau.

A cikin shekara biyar da suka gabata an kashe shugabannin kungiyar Miyetti Allah guda bakwai a sassan daban-dabna na Najeriya. Legit Hausa ta jero muku sunayensu.

An samu tashin hankali bayan barkewar fadan Fulani da Manoma a jihar Jigawa. Mutane sun riga mu gidan gaskiya yayin da aka raunata wasu mutum hudu.

Shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo ya shigar da kara kan tsare shi da aka yi ba tare da gurfanarwa ba. An kama shi bayan rikici tsakanin Fulani da tsohon soja.

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci a saki shugaban Miyetti Allah, Beloo Badejo da gaggawa. Majalisar ta bukaci Hafsun tsaro ya gurfana a gabanta.
Fulani Makiyaya
Samu kari