Wahalar man fetur a Najeriya
A labarin nan, za a ji yadda yajin aikin da kungiyar manyan ma'aikatan wutar lantarki PENGASSAN ya fara taba sassa daban-daban na kasar nan, ana cikin zullumi.
Kungiyar PENGASSAN ta ce zaman lafiya zai dawo, kuma za ta ci gaba da raba mai idan matatar Dangote ta maido da ma’aikata 800 da ta sallama kwanan nan.
Kungiyar ma’aikatan man fetur, PENGASSAN, ta rufe matatar man Dangote tare da ayyana yajin aikin kasa baki daya bayan sallamar ma’aikata 800 ƴan Najeriya.
Kumgiyar dillalan man fetur ta Najeriya watau IPMAN ta ce da yiwuwar mai ya kara tsada sakamakon matakin Dangote na daina ciniki da kudin kasar nan.
A labarin nan, za a ji yadda hamshakin dan kasuwa, Femi Otedola ya caccaki DAPPMAN da ke neman zunzurutun kudi, N1.5trn a hannun matatar Dangote.
Majiyoyi sun tabbatar mana da cewa matatar Alhaji Aliko Dangote ta dakatar da sayar da kayayyaki ga ’yan kasuwa marasa rajista daga 18 ga Satumbar 2025.
Hamshakin attajiri kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya dauki babbar kasada wajen gina matatar mai.
Dangote ya fitar da manyan motocin CNG sama da 1,000 don fara rarraba man fetur kai tsaye, zai rage farashi zuwa N820. IPMAN ta ce tana jiran isowar motocin.
Wata sabuwar rigima ta sake barkewa tsakanin Dangote da kungiyar (NUPENG), kwanaki kadan bayan da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shiga tsakani don sulhu.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari