Wahalar man fetur a Najeriya
Majiyoyi sun ce farashin danyen mai ya fadi zuwa kasa da dala $60 kan kowace ganga karo na farko tun watan Fabrairun shekarar 2021 wanda ya rikita kasuwanni.
Yan kasuwa masu zaman kansu da ke da rumbunar ajiyar fetur sun fara bin aahun Dangote wajen rage farashi, ana tsammanin litar fetur za ta dawo kasa da N800.
Matatar hamshakin dan kasuwa kuma attajirin lamba daya a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ta yi rangwame a farashin kowace elitar man fetur ana shirin kirismeti.
'Yan Najeriya sun rage sayen man fetur a Nuwamba, 2025, inda aka sayi iya lita biliyan 1.59 duk da karin samarwa da man da aka samu daga matatar Dangote.
Shugaban matatar man Dangote kuma hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, ya ba da tabbacin cewa dogon layin neman man fetur ya zama tarihi a Najeriya.
Farashin man fetur ya sauka zuwa N840 a matatar Dangote da wasu manyan dillalan Najeriya bayan saukar farashin gangar danyen man Brent zuwa kusan $62.
Rahoton NMDPRA ya nuna cewa a Oktoba 2025 matatar Dangote ta samar da lita miliyan 512 na fetur kacal, lamarin da ya tilasta ƙasar ta dogara da shigo da man fetur.
Kamfanin Dangote ya bayyana cewa raguwar farashin man fetur da ’yan kasuwa suka yi ya biyo bayan rangwamen da suka yi ranar 6 ga watan Nuwambar 2025.
Kungiyar IPMAN, ta 'yan kasuwar mai ta ce sayen fetur kai tsaye daga Dangote zai sa farashin mai ya sauka a gidajen mai a fadin Najeriya. Ta yi korafi da NMDPRA.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari