Yaki da ta'addanci a Najeriya
An kashe mutane sama da 20 a wani hari da aka kai ƙauyen Binper a Mangu, Plateau, yayin da wasu suka samu raunuka kuma ake neman mutanen da suka ɓace.
A labarin nan za a ji jihohin Najeriya da ke kan gaba wajen warewa da kashe kudi a kan matsalar tsaro a yayin da jama'a ke kara kuka da ta'addanci.
A baya, mun kawo labarin cewa rundunar sojin Najeriya ya kai daukin gaggawa zuwa jihar Zamfara inda yan bindiga suka budewa matafiya wuta da zummar sace su.
A baya, mun wallafa cewa dakarun sojin Najeriya sun gano cewa akwai sauran yan ta'adda da ke rakabe a kusa da kauyen jihar Sokoto bayan wani hari.
A labarin nan, za a ji cewa Najeriya ta bayyana cewa ta yi shirin fara kera makaman da za ta yi amfani da su wurin fatattakar yan ta'adda da suka addabi jama'a.
Matawalle ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Masar domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro, kera kayan aikin soji da yiwuwar samar da harsasai a Najeriya.
Mataimakin Gwamnan Katsina Faruk Jobe ya ce kananan hukumomi 26 daga cikin 34 na jihar na fuskantar hare-hare a 2023, amma tsaro ya inganta sosai tun daga lokacin.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu damar kwance wani bam da aka dasa a hanyar jihar Zamfara da zummar hallaka bayin Allah matafiya.
A labarin nan za a ji cewa hukumar SEC ta dauki mataki a kan mutane uku da wasu kamfanoni da ake zargin cewa su na daukar nauyin yan ta'adda a kasar nan.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari