Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa akalla ƴan bindiga 20 ne suka bakunci lahira a lokacin da faɗa ya kaure tsakanin kungiyoyi biyu da safiyar ranar Laraba a Katsina.
'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da wasu manoma a jihar Borno. 'Yan ta'addan sun hallaka mutane biyar tare da wani jami'in tsaro.
Jami'an rundunar ƴan sanda reshen jihar Akwa Ibom sun yi nasarar damke wani dagacin kauye da wasu mutum 12 da ake zargi da kisan mafarauta bayan sace su.
A wannan labarin, za ku ji cewa wani dan bindiga, Kachalla Gajere ya kashe rikakken jagoran yan ta’adda, Kachalla Tsoho Lulu a wata arangama da ta afku a Zamfara.
Kungiyar masu kishin jihar Zamfara sun karyata labarin fara zaman kotu kan zargin tsohon gwamnan jihar, Dr. Bello Matawalle da alaka da ta'addanci.
Rundunar sojojin haɗin guiwa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi ta tabbatar da miƙa wuyan wani kwamandan Boko Haram, Bochu Abacha a Borno.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce nan gaba kadan matsalar rashin tsaro za ta fi karfin gwamnati matukar ba a dauki matakin kawar da talauci ba.
S labarin nan, rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana nasarar damke wani jami'in hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) bisa alaka da yan ta'adda
A wannan labarin, jami'an tsaron kasar nan sun samu gagarumar nasara a yakin da su ke na kawar da manyan yan ta'adda daga doron kasa, inda aka kashe Kachalla.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari