Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun yi ajalin mutum 5 a wani mummunan hari da suka kai kauyen Dayau da ke Kaura Namoda a Zamfara.
Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ce gwamnatinsa ta tattara bayanan da ke nuna ƴan adawa na da hannu a hare-haren da ƴan bindiga ke yawan kai wa kwanan nan.
A wannan rahoton, gwamnatin tarayya ta ce jama'a sun fara ganin ayyukan dakarun sojojin kasar nan wajen korar yan ta'addan Lakurawa daga Najeriya.
Ministan tsaron Najeriya ya ce dakarun sojojin Najeriya sun fara fatattakar ƴan ta'addan Lakurawa, waɗanda suka fara kai hare-hare a jihohin Kebbi da Sokoto.
Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba sojoji za su shafe babin ƴan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Wasu mazauna Kaduna sun bayyana cewa yan ta'adda na neman karar da su yayin da su ka matsa da kai masu hare-hare tare da hallaka jama'a ba dare ba rana.
A wannan rahoton za ku ji cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya maka wasu fitattun yan jaridu a Arewacin kasar nan a gaban kotu bisa zargin bata masa suna.
Tsohon daraktan hukumar tsaron farin kaya watau DSS, Mike Ejiofor ya baygana cewa kungiyar ƴan ta'adda ta Lakurawa da sabuwa ba ce, ya faɗu yadda suka shigo.
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna, Shehu Sani ya ji dadin yadda ofishin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro ke gudanar da aikinsa a kasar nan.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari